Rashin tsaro a Iraki
November 22, 2007Talla
Wasu mutane a Iraƙi da ake zargi ´ Yan ƙungiyyar Al-Qaeda ne sun halaka mutane 22. Harin daya wakana a kudancin birnin Bagadaza, ya kuma yi ajalin sojin Iraƙi biyu. Tsagerun sun kuma yi amfani da motar sojin na Iraƙi, wajen kai wani harin a yankin Doura dake kudancin birnin na Bagadaza. Babu dai rahoton asarar rai ko kuma jikkata sakamakon wannan hari.