1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tabbas kan zaman lafiya a Mali

August 28, 2015

Shirin zaman lafiyar arewacin Mali da na Sudan ta Kudu da kuma hangen kawo karshen cutar Ebola na daga cikin labaran Afirka da jaridun Jamus suka duba a wannan makon.

https://p.dw.com/p/1GNVn
Mali - Rebellgruppe CMA
Hoto: Getty Images/H. Kouyate

A labarinta mai taken shirin zaman lafiya a arewacin Mali ya gamu da cikas, jaridar Die Tageszeitung cewa ta yi 'yan tawayen Abzinawa sun ba da sanawar cewa shirin tsagaita wuta ya ruguje sannan sai ta ci gaba kamar haka.

Kimanin watanni biyu bayan da gwamnatin Mali da kungiyoyin 'yan tawayen Abzinawa a arewacin kasar suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, yanzu an koma fagen yaki. Jaridar ta ce a ranar Litinin kungiyar Abzinawa ta CMA da ke fafutukar nema wa yankin Azawad 'yancin ta daina aiwatar da ka'idojin yarjejeniyar zaman lafiyar. Dalilin daukar wannan matakin shi ne fadan da ake yi a arewacin Malin tsakanin kungiyar Abzinawa mai gwagwarmayar nemawa yankin 'yanci da wasu sojojin sa kai na yankin da ake zargi na goya wa gwamnatin birnin Bamako baya. Yanzu hannun agogo ya koma baya a kokarin wanzar da zaman lafiya a arewacin kasar ta Mali mai fama da rigingimu.

Kyakkyawan fatan kawo karshen cutar Ebola

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung a wannan makon ta leka kasar Saliyo tana mai cewa an hango karshen cutar Ebola mai saurin kisa, bayan da aka sallami majinyaciya ta karshe daga wani asibiti a Saliyon.

Liberia Ebola
Ma'aikatan jinya da ke kula da masu dauke da kwayar EbolaHoto: Brot für die Welt/Christoph Püschner

Jaridar ta ce sanyen da fararen tufafi, Adama Sankoh ta rera waka ta kuma cashe lokacin da take barin cibiyar kwantar da masu fama da cutar Ebola da ke garin Makeni. Ita dai Adama Sankoh ita ce maijinyar Ebola ta karshe da aka yi rajistarta a kasar. Sallamarta daga asibitin a ranar Litinin ta zamo ranar farko na kidayar tsawon ranaku 42 kafin a hukumance Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana kawo karshen cutar Ebola a wata kasa. Sharadi dai a nan shi ne idan ba a samu sabbin wadanda suka kamu da kwayoyin cutar a tsukin wadannan kwanaki ba.

Rashin tabbas ka dorewar shirin sulhu a Sudan ta Kudu

Sudan ta Kudu ta kauce wa takunkuman Majalisar Dinkin Duniya, inji jaridar Süddeutsche Zeitung tana mai cewa ko da yake shugaban kasar Salva Kiir ya sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya bisa matsin lambar kasashen duniya amma yana da ja ga ka'idojin yarjeniyar.

Südsudan - Unterzeichnung des Friedensvertrags von Salva Kiir
Salva Kiir lokacin rattaba hannu kan yarjejenyiar zaman lafiyaHoto: Reuters/J. Solomun

Ta ce masu shiga tsakani sun kokarta inda ma shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya bayyana sanya hannu da wata rana muhimmiya ga yankin. Sai dai masu shiga tsakanin sun kasa hana shugaban na Sudan ta Kudu Salva Kiir furta kalaman rashin jin dinsa da suka biyo bayan sanya hannu kan yarjejeniyar da ya ce tana da burin canji gwamnati a kasarsa, kuma yarjejeniyar ba littafin Bible ba ne ko Al Qur'ani, ma'ana ba dole ne a yi aiki da ka'idojinta ba.

Samar da wayoyin Smartphones ga Afirka

Kamfanin Google ya kuduri aniyar bunkasa harkokinsa a nahiyar Afirka injin jaridar Neues Deutschland.

Ta ce kawo yanzu kasar China ta mamaye kasuwannin Afirka da sabbin wayoyin salula samfurin Smartphones, amma yanzu kamfanin Google na wani aikin gwaji a tarayyar Najeriya kan samar da wayoyin salula da za a kera su musamman don biyan bukatun al'ummomi a kasashe masu tasowa. Kasuwannin wayoyin salula na bunkasa kwarai a nahiyar Afirka, sai dai bukatar samun wayoyin salular masu inganci daga sanannun kamfanoni ba ta da yawa, saboda tsadarsu. Amma bisa ga dukkan alamu za a samu canji idan kamfanin Google ya fara kera wayoyin salular a Afirka.