1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tabbas kan sakamakon zaben Kenya

Abdullahi Tanko Bala
October 30, 2017

Hukumar zaben Kenya na shawarta yadda za ta yi da mazabu 25 a gundumomi hudu wadanda ba'a gudanar da zaben a cikinsu ba.

https://p.dw.com/p/2mioW
Kenia Wahlwiederholung Uhuru Kenyatta
Hoto: Reuters/S. Modola

Ana sa ran hukumar zaben Kenya a yau Litinin za ta yanke shawara ko za ta sake gudanar da zabe a wuraren da ba a yi zaben ba saboda rikici ko kuwa za ta baiyana Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe zaben.

Yayin da aka kammala kidayar kuri'un zaben shugaban kasar da aka sake gudanarwa, jami'ai na shawarta yadda za su yi da mazabu 25  a gundumomi hudu wadanda ba'a gudanar da zaben a cikinsu ba 

A waje guda kuma wani babban jami'in tsaro a Kenya ya zargi shugabannin adawa da haddasa tarzoma da kuma kaiwa 'yan sanda hari yayin zaben shugaban kasar da aka sake gudanarwa.

Martin Kimani mai baiwa shugaban kasar shawara kan ayyukan ta'addanci ya shaidawa 'yan jarida cewa zanga zangar da suka wakana sun samo asali ne daga kalaman tunzuri na 'yan siyasa na bangaren adawa musamman madugun adawar Raila Odinga.

Akalla mutane shida suka rasu a ranar Alhamis a lokacin zaben.