1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin tabbas bayan zaben raba gardama a Birtaniya

Abdul-Raheem HassanJune 27, 2016

Majalisar dokokin Birtaniya ta yi zama na farko tun bayan da kasar ta kada kuri'ar amincewa da fita daga Tarayyar Turai domin mahawa kan abin da zai biyo baya.

https://p.dw.com/p/1JEZG
England Parlamentssitzung Premierminister David Cameron
Hoto: Reuters/UK Parliament

Tun dai bayan zaben raba gardama da mutanen Birtaniya suka yi na fita daga Tarayyar Turai a makon jiya, siyasar kasar na dauki sabon salo. A gefe guda kuma manyan kasashe a kungiyar Tarayyar Turai na ci gaba da mahawara kan matsayar Birtaniyar.

Yayin da Birtaniya ta yi zaben raba gardama da zai janyo raba gari da kungiyar Tarayyar Turai ke zama abin da ke ci gaba da jan hankalin duniya. Kawo yanzu dai tuni shakku da rashin tabbas suka soma tasiri a ciki jam'iyyun kasar. Kana a karon farko Firaminista David Cameron ya bayyana a gaban majalisar dokokin Birtaniyar inda ya yi bayani a kan yadda ballewar kasar daga Tarayyar Turai zai kasance. Sannan ya nemi a rungumi abin da ya faru da karfin gwiwa.

Symbolbild England Brexit Boot mit Union Jack
Hoto: picture-alliance/dpa/E. S. Lesser

A daya hannun cikin wata sanarwa da kwamitin gudanarwar jam'iyyar Conservative da ke mulki a Birtaniyar ta ce za a kaddamar da shirye-shiryen zaben maye gurbin Firaminista David Cameron kuma za a sanar da sabon shugaban jam'iyyar ranar biyu ga watan Satumba da ke tafe. Amma wani batu da ya dauki hankali a Birtaniya shi ne yadda 'yan kasar ke yi wa baki barazanar kora tun bayan zaben, abin da mahukunta suka ce ana bin matakan da suka dace domin dakile matsalar.

London Protest Anti Brexit Rassismus Flüchtlinge
Hoto: picture-alliance/Photoshot/H. Yan