Rashin jituwa tsakanin kungiyoyin Hamas da Fatah a Falasdinu | Labarai | DW | 27.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rashin jituwa tsakanin kungiyoyin Hamas da Fatah a Falasdinu

Kungiyoyin Falasdinawa dake gaba da juna wato Hamas da Fatah sun jinkirta gudanar da shawarwarin da aka shirya farawa yau asabar inda za´a tattauna kan wani shiri wanda ya yi kira da kafa kasar Falasdinu mai makwabtaka da Isra´ila. Kakakin kungiyar Hamas Sami Abu-Zuhr ya ce ba bu bukatar wani wa´adi na kwanaki 10 da shugaba Mahmud Abbas ya bayar na a amince da wannan shiri ko kuma ya kira kuri´ar raba gardama a cikin kwanaki 40. Shirin dai ya amince da wanzuwar kasar Isra´ila, amma manufofin kungiyar Hamas na kira ne da rusa kasar ta Bani Yahudu. A wani labarin kuma daruruwan sojojin sa kai na Hamas sun koma kan titunan Zirin Gaza a yau asabar, kwana daya kacal bayan an janye su a wani mataki na kawo karshen wani artabu da yayi sanadiyar mutuwar mutane 10 a makon da ya gabata.