Rashin imani da juyayi da kuma firgici.
Hari da wata babbar mota a kasuwar Kirsimeti a Berlin. Mutane 12 sun rasa rayukansu, kana wasu kusan 50 sun jikkata. Wannan mummunan hari ya haifar da fargaba tsakanin kasashen duniya.
Washegari bayan harin
Mutane cikin dimuwa na wucewa ta wurin da aka kai harin. Wasu na ajiye furanni wasu kuma na kunna wutar kandir. Ma'aikatar harkokin cikin gida ta ayyana zaman makoki na kasa baki daya.
Ana hallara a Coci domin adduo'i
Mujami'ar Berlin ta samu halartar masu adduo'i ga wadanda suka mutu. Kazalika an sake bude mujami'ar Kaiser-Wilhelm da ke unguwar da aka kai mummuna harin, kuma Limaman coci na yi wa mutane bayani. A yayin da majalisar dattijai ta bude littafin gaisuwar ta'aziyya.
Babbar mahada
"Har yanzu kuna tare da mu". Abun da wasu mazauna babban birnin suka rubuta kenan a kan wata takarda da aka ajiye tare da Furanni.
An rufe kasuwar Kirsimeti ta Berlin
Kasuwar Kirsimeti ta Breitscheidplatz na cigaba da kasancewa a rufe. Hukumomin Berlin sun yi kira ga sauran masu shaguna a sauran kasuwannin Kirsimeti da su kasance a rufe ranar Talata don tunawa da 'yan uwa da suka mutu.
An tsaurara matakan tsaro a kasuwannin Kirsimeti
Za'a ci gaba da gudanar da kasuwannin Kirsimeti a fadin Jamus, kamar yadda ministan harkokin cikin gida na tarayya da na sauran jihohi suka tabbatar a tattaunawarsu ta wayar tarho. Sai dai wajibi ne a kara tsaurara matakan tsaro.
Hadin kai a duk duniya
Akwai kamarori na kafofin yada labaru na kasashe daban-daban a gaban inda aka kai harin.Labarin harin na Berlin dai ya mamaye kafafen sadarwa na duniya. A hirar su ta wayar tarho da shugabar gwamnati Angela Merkel, shugaba Barack Obama na Amurka ya yi alkawarin bada hadin kai dangane da binciken harin.
Labarin ya mamaye kafofin sada zumunta na Internet
Kazalika a shafukan sada zumunta kamar Facebook da Twitter, harin na Berlin ya kasance babban labari. Mutane sun nuna juyayi da goyon bayansu ga al'ummar Berlin. Kamar yadda ya kasance a ranar 14 ga watan Juli a birnin Nice, lokacin da wani mahari ya bi ta kan mutane da mota.
Merkel: Ba zamu lamunta ba
Shugabar gwamnati ta ce harin mugun abu ne da ba za a lamunta ba. Kuma za a dauki mataki na hukunci kamar yadda dokar kasa ta tanada ga wanda ke da hannu. Merkel ta yi kira ga jama'a da su cigaba da rayuwar walwala ba tare da fargaba ba.
Karin 'Yan sandan sintiri
Sanye da riguna masu sulke, dauke da manyan makamai, jami'an tsaro na ci gaba da sintiri a wurin harin. A wani mataki na kasancewa cikin shirin ko ta kwana, hukumomi a Berlin sun sanar da tsaurara matakan tsaro.