1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin fahimtar juna a tsakanin Russia da Ukraine

December 29, 2005
https://p.dw.com/p/BvEd

An kammala taron wakilan kasar Russia dana kasar Ukraine ba tare da cimma matsaya guda ba, a game da matakin kara farashi a kann hayakin gas da kasar Russia take sayarwa kasar ta Ukraine.

Kamfanin samar da hayakin gas din na Russia, wato Gazprom yace daga daya ga watan Janairun sabuwar shekara zai tsayar da hayakin gas din da yake sayarwa kasar ta Ukraine, matukar basu yarda da matakin karin farashin ba .

Idan dai za a iya tunawa, an tashi daga irin wannan tattaunawa da aka gudanar a jiya laraba ba tare da tsinana komai ba, a tsakanin ministan makamashi na kasar ta Ukraine da takwaran sa na Russia.

Ya zuwa yanzu dai tuni, shugaba Vladimir Putin na Russia yace, kasar sa a shirye take ta bawa kasar ta Ukraine bashin dala miliyan uku da digo shidda don samun damar cike gibin kudaden hayakin na gas da suke saya daga kamfanin na Grazprom.