1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Rashin daidaito a tsarin ba da ilimi a Jamus

Duk da jerin sauye sauye da aka yi a tsarin ilimi a Jamus, har yanzu babu daidaito wajen ba da ilimin, saboda bambamcin tallafi ga yaran makaranta.

Manfred Prenzel mai binciken harkar ilimi ne kuma mai ba wa gwamnatin tarayyar Jamus shawara. A wani lokaci ya kan gabatar da labarai marasa daɗin ji. Alal misali a farkon watan Afrilu ya sanar da kwamitin ilimi na majalisar dokoki ta Bundestag cewa akwai babbar matsalar rashin daidaito a Jamus. "Tallafin da 'yan makaranta ke samu ya danganci jihar da su ke, saboda jihohin tarayyar na tafiyar da manufofin ilimi mabambamta." Abin nufi yaron dake zuwa makaranta a jihohi kamar Bremen ko Schleswig-Holstein yana da naƙasu idan aka kwatanta shi da wanda ke makaranta a jihohin Baveriya ko Saxony. Sai dai sha'anin ilimi a Jamus mai bin tsarin tarayya, harka ce da ta shafi gwamnatocin jihohi, inda kowace jiha ke bin manufofin da suka fi dacewa da ita kuma za ta iya ɗaukar nauyinsu. Saboda haka shaidar shiga jami'a daga jihar Baden-Württenberg ta fi ta Berlin daraja.

Baya ga haka wani abin da ke taka rawa kuma shi ne makarantar da yaro yake da kuma gidan da ya fito. Wani bincike a kan "Matsayin Damarmaki" da gidauniyar Bertelsmann ta yi baya bayan nan ya tabbatar da haka a fili. Yaron da ya tashi daga unguwar talakawa ko ya fito daga iyayen da ba su da ilimi ko iyayensa baƙi ne 'yan ci-rani, ba shi da kyakkyawar dama ta samun ilimi ingantacce, idan aka kwatanta shi da yaron da iyayensa suka yi jami'a ko ya taso daga unguwannin 'yan ƙasa masu hannu da shuni. Wannan wani sakamako ne mai baƙanta rai dake da illa babba, domin ba sabon abu ba ne. Tun kimanin shekaru goma da suka gabata ya kamata a ce an kawar da shi ta hanyar sauye sauye a faɗin tarayya.

ILLUSTRATION - Ein Lehrer schreibt die Wörter PISA Studie am Montag (06.12.2010) an einer Hauptschule in Arnsberg (Sauerland) auf eine Glasscheibe, während Schüler im Unterricht sitzen. Fast eine halbe Millionen 15-Jähriger machte mit. Am Dienstag wird die neue Studie vorgestellt. Foto: Julian Stratenschulte dpa/lnw +++(c) dpa - Bildfunk+++

Tsarin ba da ilimi a Jamus ya daɗe a matsayin ingantaccen tsari. Ba a taɓa saka ayar tambaya game da darussa da rarraba 'yan makaranta da wuri tun bayan firamare zuwa makarantun sakandare na matakin ilimi dabam-dabam ba.

Sakamakon PISA ya kaɗa hukumomin Jamus

Amma a shekarar 2001 bayan bayyana sakamakon nazarin farko na PISA, wato nazarin ingancin ilimin makarantu na ƙasa da ƙasa da ƙungiyar haɗin kan tattalin arziki da ci-gaba wato OECD ta yi, gwamnatin tarayyar Jamus ta nuna kaɗuwarta. Domin an ba wa tsarin ilimin makarantun Jamus mummunar daraja. Musamman a fannonin karatu, lissafi da kimiyya, yaran makarantar Jamus 'yan shekaru 15 da suka yi wannan jarrabawa, sune a sahun ƙarshe idan aka kwatanta da takwarorinsu na ƙasashe masu ci-gaban masana'antu. Wani batun da ya fi tayar da hankali shi ne Jamus ce ƙasar da asalin yaro ya fi taka rawa wajen ƙoƙarinsa a makaranta, wato babu ƙasar da yaran baƙi suka zama na baya ga dangi a makaranta da ta kai Jamus. Shi ya sa a nan ba a maganar damarmaki daidai wa daida.

Tun bayan wannan nazarin ake kwan gaba kwan baya wajen aiwatar da sauye sauye. Ko wace jiha da na ta tsari, amma a kan buri ɗaya wato inganta tsarin ba da ilimi don samu kyakkyawan sakamako da ƙara yawan yara dake shiga jami'o'i ba tare da la'akari da asalinsu ba. Manufa ita ce samar da wata jamhuriya ta ilimi wadda duk da ƙarancin albarkatun ƙarƙashin ƙasa, za ta kasance jagora a fannin tattalin arziki wadda ta dogara a kan haziƙai da ƙirƙiro sabbin ababa na ci-gaba. Tun a matakin nasare ilimi ya zama muhimmin batu, tun yaro yana shekara biyar da haihuwa ake tura shi firamare, sannan bayan turjiyar da aka fuskanta da farko, an samar da makarantu da ya wa na yini gaba ɗaya a dukkan faɗin tarayyar Jamus. Ana koyar da darussa dabam dabam har da iya ƙirƙire ƙirƙire da tallafa wa ɗaiɗaikun 'yan makaranta. Bambamcin ƙarfin ilimin ɗan makaranta ba ya farawa a aji na huɗu na firamaren, sai daga baya. A halin da ake ciki matsayin ilimin yaran makarantar Jamus 'yan shekaru 15 ya inganta, musamman a fannonin karatu, lissafi da kimiyya a jerin ƙungiyar OECD. Hakazalika yawan masu samun damar shiga jami'a ya ƙaru. Amma ba a samu daidaiton damarmaki ba.

Har yanzu ba ta canza zane ba

Abubuwa da dama ba su canja ba. Har yanzu ana rashin ƙwararrun malamai, har yanzu akwai ƙarancin kuɗin da ake buƙata kuma har yanzu batun gogayya na ci-gaba da mamaye tsarin ilimi a Jamus. Wasu jihohin tarayya na gogayya tsakaninsu game da nasarar ilimi, kamar wasu birane da ƙananan hukumomi, hakazalika wasu ɗaiɗaikun makarantun suna gogayya tsakaninsu. Ba sa fuskantar wata alƙiblar ilimi iri guda, ko wace na da fannin da ta fi ba wa fifiko. A wasu makarantun fasaha da waƙe ke kan gaba, wasu kimiyya da fasaha suka fi ba wa fifiko, yayin da a wasu makarantun ake ba wa 'ya'yan baƙi ƙarin darasin koyan Jamusanci, wasu kuma harsunan Rasha da China suke koyarwa. A wasu lokutan ma makarantun na zama tamkar wuraren kariya ga zamantakewa. Duk wanda ya yi karatun mun natsu zai samar wa kansa da ɗansa makaranta mafi dacewa. Saura kuwa sai dai su zama 'yan kallo.

Mawallafa: Silke Bartlick / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu

Karin shafuna a WWW