1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin agaji ya nakasa yara a Nijar

August 8, 2017

Likitocin karkara a Nijar sun bayyana fargaba kan yankewar abinci ga yara kanana da ke fama da matsalar cutar tamowa da asusun kula da abinci na majalisar dinkin duniya ke bayarwa tsawon watanni uku baya.

https://p.dw.com/p/2hsjH
Afrika Hungerkatastrophe Archivbild 2005
Hoto: picture-alliance/dpa

A yankin Damagaram na Jamhuriyar Nijar wasu likitocin yankunan karkara ne suka bayyana fargabansu game da katsewar tallafin abinci da sanadarai masu gina jiki ga yara kanana da ke fama da matsalar cutar tamowa da asusun kula da abinci na majalisar dinkin duniya ke bayarwa  tsawon watanni uku baya.

Hungernde Zivilisten Mali
Hoto: AFP/Getty Images

A cewar likitocin garin Kiringim da ke cikin gundumar Goure, matsalar na kara kamari ne ta la'akari da irin yadda adadin masu fama da cutar ke karuwa tsakanin iyaye masu baikon nono a sakamakon katsewar tallafin. Mataimakin shugaban asibitin Kiringim, Mahaman Alhaji Garba Aji, ya tabbatar da munin lamarin ganin yadda ya fara tasiri a rayuwar al’umma. Wani Uba da wakilin DW ya zanta da shi a kan wannan matsala ta tamowa a karkarar makiyayan ya yi korafi tare da bayyana irin yadda za su cike gurbi ko akasin haka.

Ana dai ganin bambanci a jikin yara da ma iyayensu duba da halin da suke ciki a matsayinsu na mazauna dazukan kiwo da suka yi nisa da kasuwanni, musamman a irin wannan lokaci na faduwar farashin dabbobi da a kansu ne suka dogara wajen samun kudade. Bayan matsalar cutar ta tamowa dai likitotin sun koka da matsalar motocin daukar marasa lafiya da shi ma ke zaman wani babban kalubale a lokutan da ayyukan gaggwa ke tasowa.