Rasha zata ba wa Falasdinawa taimakon kudi da su ke bukata cikin gaggawa | Labarai | DW | 15.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha zata ba wa Falasdinawa taimakon kudi da su ke bukata cikin gaggawa

Rasha ta ce zata ba da wani taimakon gaggawa don rage radadin matsalar karancin kudi da gwamnatin Falasdinawa karkashin jagorancin kungiyar Hamas ke fuskanta. An jiyo haka ne a cikin wata sanarwa da ma´aikatar harkokin waje a birnin Mosko ta bayar ba tare da ta bayyana yawan taimakon ba. A lokaci daya kuma Rasha ta yi kira ga kungiyar Hamas ta Falasdinawa masu gwagwarmaya da makami da ta amince da wanzuwar Isra´ila. A cikin makon da ya gabata Amirka da KTT suka dakatar da taimakon kudin da suke ba hukumomin Falasdinu bayan da Hamas ta karbe ragamar gwamnati. A jiya juma´a gwamnatin Amirka ta haramtawa ´yan kasar da kuma kamfanoninta yin wata huldar kasuwanci da gwamnati Hamas. A wani labarin kuma shugaban addinin Iran, Ayatollah Ali Kameni ya yi kira ga kasashen musulmi da su taimakawa hukumar mulkin Falasdinu da makudan kudade. Yayi wannan kira ne a gun wani taron nuna zumunci ga Falasdinawa dake gudana a birnin Teheran.