Rasha za ta ginawa Iran tashar Nukiliya | Labarai | DW | 19.03.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha za ta ginawa Iran tashar Nukiliya

Rasha za ta kammala gina tashar nukiliyar Iran ba da jimawaba

default

Putin da Ahmadinejad

Ƙasar Rasha ta bayyana cewa yanzu ta kammala shirin fara aikin ƙarisa gina tashar nukiliyar Iran, wanda dama ta fara ginawa. Firayim ministan ƙasar Rasha Vladimr Putin yace tashar nukilyar Iran dake a Bushehr, za ta fara aiki ba da jimawa ba. Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya kare matakin inda yace hukumar kula da ƙayyade makaman nukilya ta Majalisar Ɗinkin Duniya wato IAEA tana kulawa da ayyukan nukilyar Iran, don ganin ta bi ƙa'idojin duniya. Wannan sanarwar dai ta zo ne a dai dai lokacin da sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta isa Rasha domin matsawa mahukuntan ƙasar lamba, da su jinkirta batun ginawa Iran tashar ta nukiliya, kana Clinton ta buƙaci da Rasha ta goyi bayan azawa Iran wani sabon tankunmin karya tattalin arziki. Amirka dai tana jagorantar wani mataki na azawa Iran takunkumi na huɗu, bisa manufarta ta mallakar makamashin nukliliya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman  

Edita: Abdullahi Tanko Bala