1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha: 'Yan adawa sun yi zargin magudin zabe

Ramatu Garba Baba
March 18, 2018

A yayin da ake daf da kamalla kidayar kuri'u a zaben kasar Rasha, wani madugun adawa mamalakin wani kamfani mai zaman kansa da ke sa ido kan zabe, ya ce an tafka magudi a zaben neman kujerar shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/2uXo5
Wahlen in Russland Wladimir Putin
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Hakazalika Alexei Navalny babban mai hamayya da gwamnatin Putin da aka hana wa yin takara a zaben bisa wasu hujjoji na shari'a, ya wallafa a shafinsa na yanar gizo hotunan bidiyon magudi da ya ce an aikata da akwatunan zabe. Tuni sakamakon zaben ya soma nuna cewa shugaba mai ci Vladimir Putin ke sahun gaba don lashe zaben shugabancin kasar a sabon wa'adin mulki karo na hudu.

Rahotannin na nuni da cewa bayan kidayar kashi saba'in cikin dari na kuri'un da aka kada, shugaba Putin na sahun gaba daga cikin 'yan takara bakwai da suka fafata a kokarin samun nasara dare kujerar mulkin kasar.