Rasha tayi gwajin makamai masu Linzamin isa wata Nahiya | Labarai | DW | 08.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha tayi gwajin makamai masu Linzamin isa wata Nahiya

A yau ne Rasha tayi nasarar gwajin makamanta masu Linzami ,da zasu iya lalata naurar kare makamai masu linzami ,wadanda kuma zaa iya harba su zuwa wata nahiya.Da yammacin yau ne dai Rashan ta gudanar da gwajin makamin nata na RS-12M Tapol,wadda NATO ke kira SS-25 Sickle,a yankin kudancin kasar cikin nasara.Kakakin rundunar dake kula da makaman kasar Alexender Vovk ya fadawa kamfanin dillancin labarun Rashan cewar,an kaddamar da makaman ne da nufin tabbatar da irin tasirin da wannan irin makami mai Linzami zaiyi ta sararin samaniya,bayan an harba shi.Kazalika Gwajin nada nufin ,ganin yadda makamin zai iya tarwatsa nasu’rar kare makamai masu Linzami.Tuni dai Shugaba Vladimir Putin yace yunkurin Amurka na dasa naurorin kare makamai masi linzami a turai,zaiyi barazana wa harkokin kasarsa .