1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha tace zata fice daga yarjejeniyar makamai da nahiyar turai.

July 14, 2007
https://p.dw.com/p/BuGO

Shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin ya sanya hannu a kan wata doka wadda zata tsame ƙasar Rashan daga shiga wasu muhimman yarjeniyoyi da tarayyar turai dangane da taƙaita makamai. Fadar gwamnatin Kremlin ta baiyana ficewa daga yarjejeniyar da tarayyar turan wanda aka fi sani da CFE a taƙaice, wanda aka tsara da nufin taƙaita yawan manyan makamai a nahiyar. Kakakin kungiyar tsaro ta NATO a birnin Brussels James Appathurai yayi Allah wadai da matakin da Rasha ta ɗauka, yace wannan babban abin takaici ne kuma gurguwar shawara ce mahukuntan Rashan suka ɗauka domin ko kaɗan bai dace ba. A nata ɓangaren Mosco ta ce zata fice daga yarjejeniyar ce saboda gazawar yammacin turan ta aiwatar da sabon daftarin yarjejeniyar wadda suka amince da ita a shekarar 1999. Amurka da ƙungiyar tarayyar turai sun buƙaci Rasha ta janye sojojin ta daga Moldova da Georgia dake tsohuwar tarayyar Soviet kafin su sanya hannu akan yarjejeniyar.