Rasha tace bata tabbatar da ko jamianta aka kashe ba a Iraqi | Labarai | DW | 26.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha tace bata tabbatar da ko jamianta aka kashe ba a Iraqi

Kasar Rasha tace har yanzu bata tabbatar da kashe jamian diplomasiyanta guda 4 a kasar Iraqi ba.

Ministan harkokin cikin gida Sergei Lavrov yace akwai shakku game da tabbacin hotunan bidiyo da aka aike ta shafin internet dake nuna yadda aka kashe wasu mutane su 3.

Hotun dai ya nuna wasu mutane da fuskar take rufu suna fille kan wani mutum guda daya kuma aka harbe shi,tare kuma da nuna gangan jikin mutum na uku.

Ministan harkokin wajen rashan yace gwamnatinsa bata da tabbaci dari bisa dari cewa,wadannan mutane jamian ta ne da suka bace,a farkon wannan wata a birnin Bagadaza.