Rasha ta zargi ƙasar Georgia da gudanad da ayyukan ta’addanci. | Labarai | DW | 01.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta zargi ƙasar Georgia da gudanad da ayyukan ta’addanci.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya nuna matuƙar ɓacin ransa ga rikicin diplomasiyyan da ya ɓarke a halin yanzu a ƙasar Georgia. Ya ce kame hafsoshin Rashan guda 4 da jami’an Georgian suka yi a ran larabar da ta wuce, saboda zargin da suke yi musu na leƙen asiri, wato gudanad da ayyukan ta’addanci da kuma yin garkuwa da mutane ne da mahukuntan ƙasar gaba ɗaya ke yi. A jiya asabar ne dai Rashan ta janye duk jami’an diplomasiyyanta daga ƙasar ta Georgia.