Rasha ta yi kira ga Syria da ta ba da cikakken hadin kai a binciken kisan Hariri | Labarai | DW | 26.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta yi kira ga Syria da ta ba da cikakken hadin kai a binciken kisan Hariri

Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya yi kira ga Syria da ta bawa jami´an MDD dake binciken kisan gillar da aka yiwa tsohon FM Lebanon Rafik Hariri cikakken hadin kai. A lokaci daya mista Lavrov ya ce bai kamata a sanya wata manufa ta siyasa a cikin binciken ba. A wata hira da yayi da takwaransa na Syria Farouk al-Sharaa ta wayar tarfo, Lavrov ya ce ya zama wajibi dukkan wadanda abin ya shafa ciki har da Syria da su ba jami´an binciken na MDD cikakken hadin kai. Yanzu haka dai Syria ta amince masu bincken na MDD karkashin jagorancin mai shigar da kara na Jamus Detlev Mehlis su yiwa jami´anta tambayoyi a game da kisan na Hariri a birnin Vienna. Syria ta saduda ne sakamakon matsin lamba da ta sha daga ketare. A kuma halin da ake ciki gwamnatin Lebanon ta yi lale maraba da wannan amincewa da Syria ta yi game da yi wa jami´an leken asirin ta tambayoyi a birnin na Vienna.