Rasha ta yafewa kasashe matalauta basussukan da take bin su | Labarai | DW | 10.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta yafewa kasashe matalauta basussukan da take bin su

Kasar Rasha ta yi alkawarin yafewa kasashe matalauta na Afirka bashin dala miliyan 700. Ministan kudin Rasha Alexey Kudrin ya bayyana haka a gun taron ministocin kungiyar kasashe 7 mafiya arzikin masana´antu a duniya da kuma Rasha a birnin St. Petersburg. To amma a na su bangaren kasashen da ake bin su bashi zasu kashe dala miliyan 250 wajen yaki da cututtuka masu sauri yaduwa tare da inganta hanyoyin sadarwa musamman na samar da makamashi. Ministan ya ce an cimma yarjejeniyar yin haka tsakanin Rasha da bankin Duniya. Taron ministocin na yau na matsayin share fagen taron kolin da kungiyar G-8 zata yi a birnin St.Petersburg a tsakiyar watan yuli. Muhimman batutuwan da taron zai fi mayar da hankali a kai sun hada da samar da makamashi da kuma wani sabon shirin allurar riga-kafi ga kasashe masu tasowa.