1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta nemi zaman Kwamitin Sulhu

Salissou Boukari
April 5, 2018

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai yi zama na musamman bisa bukatar kasar Rasha kan batun saka guba da ake zargin Rasha da yi ga wani tsohon dan leken asiri na kasarta a Britaniya.

https://p.dw.com/p/2vW3q
Russland Putin bei TV-Rede
Hoto: Getty Images/AFP/M. Klimentyev

Rasha dai ba ta samu gamsar da hukumar nan da ke kula da haramcin amfani da makammai masu guba ta kasa da kasa ta OIAC na ganin ta saka Rasha a cikin harkokin binciken. Wakilin Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vassily Nebenzia ya ce Kwamitin Sulhun zai yi zama na bainar jama'a a wannan Alhamis din ce da misalin karfe uku agogon New York, karfe bakwai agogon GMT, inda ya ce Rasha na bukatar ganin cikin tsanaki, taron ya yi nazarin wasikar Firaministar Britaniya Theresa May kan zargin da ta yi wa Rasha na yunkurin kashe Sergueï Skripal, da 'yarsa Loulia ta hanyar guba.

Rasha dai ta sha nanata cewa bata da hannu cikin wannan lamari, inda ta ce kawai tsokala ce ta kasashen Yamma da kuma yada bayanai na neman bata mata suna. A ranar 14 ga watan Maris da ya gabata ma dai Kwamitin Sulhun na MDD ya yi wani zama kan wannan batu bisa tambayar kasar Britaniya.