Rasha ta ki goyon bayan daukar tsauraran matakai kan Pyongyang | Labarai | DW | 21.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta ki goyon bayan daukar tsauraran matakai kan Pyongyang

A ziyarar da sakatariyar harkokin wajen Amirka C. Rice ta kaiwa Rasha, shugabannin kasar sun nuna mata cewa ba zasu goyi da baya yin amfani da tsauraran matakai a takaddamar da ake yi da KTA akan shirinta na nukiliya ba. A ganawar da yayi da Rice, ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov yayi kira ga Amirka da KTA da su nuna sassauci. Wani kakakin Lavrov ya nunar da cewa Rasha zata aiwatar da takunkuman da kwamitin sulhun MDD ya kakabawa KTA. Dr. Rice ta kuma gana da shugaba Vladimir Putin akan matakan bai daya da za´a iya dauka kan KTA. Sakatariyar harkokin wajen ta Amirka ta kuma ziyaraci dan ´yar jaridar Rashan nan da aka yiwa kisan gilla Anna Polit-Kovskaya da wasu abokan aikinta a birnin Mosko.