1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta fara tura iskar gas zuwa Georgia

January 29, 2006
https://p.dw.com/p/BvAN

Mako daya bayan harin da aka kai kan bututun gas guda biyu, kasar Georgia ta fara samun iskar gas da take matukar bukata daga Rasha. Kafofin yada labarun Rasha sun jiyo wakilan kamfanin Gas na Rasha wato gasprom da kuma kamfanin dake kula da bututun gas din na cewa an kammala aikin gyaran bututun gas din saboda haka yanzu an fara aikewa da iskar gas zuwa kasashen Georgia da Armenia. A ranar lahadi da ta wuce wasu da ba´a gane su ba suka kai harin bam akan bututun gas din da ya ratsa cikin yankin arewacin Osetia zuwa Georgia. Gwamnatin Georgia ta zargi Rasha da katse tura mata da iskar gas din da gangan.