Rasha ta fara daukar matakan ba sani ba sabo kan kungiyoyi masu zaman kansu | Labarai | DW | 14.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta fara daukar matakan ba sani ba sabo kan kungiyoyi masu zaman kansu

Wata kungiyar da ba ta gwamnati a ba a Rasha wadda ta dukufa wajen shirya tarukan tuntubar juna tsakanin ´yan Rasha da ´yan Chechniya ta zama wata kungiya mai zaman kanta ta farko da aka haramta ayyukanta a karkashin sabuwar dokar yaki da masu tsattsauran ra´ayi. Wata jaridar Rasha ta rawaito cewa a yau asabar an rufe ofishin kungiyar ta abokan Rasha da Chechniya mai mazauni a a birnin Nizhny Novgorod dake yammacin kasar a karkashin sabuwar dokar da aka yiwa kwaskwarima. Tuni dai har kungiyar kare hakin bil Adama ta kasa da kasa wato Amnesty International ta yi tir da rufe ofishin kungiyar. A cikin wata sanarwa Amnesty ta ce sabuwar dokar ka iya ba wa hukumomin Rasha damar daukar irin wannan mataki akan sauran kungiyoyi masu zaman kansu.