1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta ce za ta dakatad da shirin janye dakarunta daga ƙasar Georgia.

Rasha ta ce za ta dakatad shirin janye dakarunta daga ƙasar Georgia. Wannan sanarwar dai ta zo ne tamkar hauhawar tsamari ta baya-bayan nan a ce-ce kucen diplomasiyya da ake yi tsakanin ƙasashen biyu tun ran larabar da ta wuce, yayin da gwamnatin birnin Tibilisi, wato ta Georgian, ta tsare wasu hafsoshin sojin Rashan guda huɗu, tare da yi musu sukar leƙen asiri. Hakan dai ya sa Moscow janye mafi yawan jami’anta daga ofishin jakadancinta da ke babban birnin ƙasar Tiblisi. Tun lokacin tarayyar Soviyet ne dai Rashan ke da dakaru girke a Georgian, kuma bisa wata yarjejeniyar da aka cim ma, da cikin shekara ta 2008 ne za su janye gaba ɗaya daga ƙasar.