1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta buƙaci a yi sulhu a Ukraine

November 17, 2014

Shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin ya yi gargaɗin cewa Moscow ba za ta zuba idanu tana kallo a murƙushe 'yan awaren da ke yankin gabashin Ukraine ba.

https://p.dw.com/p/1Dorh
Hoto: picture-alliance/dpa/Mikhail Klementyev/Ria Novosti

Putin ya bayyana hakan ne yayin da yake hira da gidan talabijin din ARD na nan Jamus inda ya ce kamata ya yi ɓangarorin biyu da ke yaƙar juna a Ukraine ɗin su zauna kan teburin sulhu domin warware matsalar da ke tsakaninsu cikin ruwan sanyi. Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ministocin harkokin ƙasashen ƙetare na nahiyar Turai ke taro a birnin Brussels, inda za su tattauna batun yiwuwar sake ƙaƙabawa Rashan takunkumi kan zargin da suke mata na iza wutar rikicin na Ukraine da kawo yanzu yai sanadiyyar mutane mutane da dama tare da asarrar dukiyoyi masu yawan gaske.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane