Rasha ta ba wa Snowden karin wa'adin zama.
August 7, 2014Mai kwarmata bayanan nan dan asalin Amirka Edward Snowden ya sake samun takardar ci gaba da zama a kasar Rasha har na tsawon shekaru 3, kamar yadda lauyan da ke kare shi ya bayyana a ranar Alhamis dinnan.
A shekarar da ta gabatane mahukuntan na birnin Moscow suka bada damar zama ga Snowden na tsawon shekara guda, wacce ta kare a ranar daya ga watannan na Agusta.
Anatoly Kucherena shine lauyan da ke kare mista Snowden:
"An dauki mataki kan takardun neman karin waadin da muka gabatar wanda daga ranar 1 ga watan Agusta na shekarar 2014 Snowden zai ci gaba da zama a wannan kasa har tsawon shekaru 3".
Tun bayan da ya samu takardar wucin gadi ta zama a wannan kasa baa sake jin labarin inda yakeba, wannnan mataki kuma na mahukuntan na Rasha ya sake rura wutar takun sakar da ke tsakaninsu da Amirka.
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Mohammad Nasiru Awal