1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha: MDD ta bincika zargin Birtaniya

April 4, 2018

Gwamnatin kasar Rasha ta bukaci kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da ya tattauna zargin da Birtaniya ta yi mata dangane da amfani da guba kan tsohon jami'in diflomasiyyarta.

https://p.dw.com/p/2vVBM
Russischer UN-Botschafter Vasily Nebenzya
Vassily Nebenzia, jakadan Rasha a Majalisar Dinkin DuniyaHoto: AFP/Getty Images/K. Betancur

Hukumar yaki da yaduwar sinadarai masu guba a duniya, wadda ta zauna a birnin Hague a yau Laraba, ta ce Rasha ta gaza samun rinjayen da ake bukata a binciken zargin amfani da guba kan tsohon jami'in diflomasiyyarta a Birtaniya. Rasha dai ta sami kuri'u shida ne, inda wakilai 15 suka ki kada kuri'unsu.

Yanzu dai Rashar ta bukaci kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da ya tattauna zargin da Birtaniya ta yi mata dangane da gubar kan tsohon jami'in diflomasiyyar. Cikin watan jiya ne Sergei Skripal tare da 'yarsa suka fuskanci hari na guba ta tsigar jiki, wadda Birtaniya ta yi zargin hadin kasar ta Rasha ce.

Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vassily Nebenzia, ya ce zaman kwamitin sulhun a gobe Alhamis, zai yi nazarin wata wasikar da Firaministar Birtaniya Theresa May ta aike wa majalisar a ranar 13 ga watan jiya, inda a ciki ta yi zargin Rashar.