1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha da Iran zasu gana domin sulhunta rikicin Nukiliya

February 20, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7Q

A yau hukumomin Iran dana Rasha zasu gana a birnin Mosco domin tattauna masalaha ta karshe da zata kai ga warware dambarwar dake tsakanin Iran da yammacin turai a game da shirin Nukiliya na kasar Iran din. Rasha ta yi tayin sarrafawa Iran makamashin Uranium din da take bukata domin samar da hasken wutar lantarki. Sai dai kuma zata sarrafa sinadarin ne a cikin kasar Rasha. Wannan ce kawai dama da ake gani zaá rage zargin da kuma damuwar da kasashen duniya ke da shi da zai hana Iran kera makamin Nukiliya. Amurka da kasashe uku na kungiyar tarayyar turai wadanda suka hada da Faransa da Britaniya da Jamus duk sun amince da shawarar ta Rasha sai dai wasu jakadu na baiyana shakku ko Iran zata amince da wannan shawara. Ita dai kasar Iran ta baiyana cewa tana da cikakkiyar dama ta aiwatar da sarrafa makamashin ta na Nukiliya a cikin kasar ta, to amma zata saurari cikakken bayanai daga Rasha a game da wannan shawarar.