Rasha da Iran sun fara tattaunawa a birnin Teheran akan takadamar nukiliya
January 7, 2006Talla
Kasashen Rasha da Iran sun fara tattaunawa a birnin Teheran akan shawarar da gwamnatin Mosko ta gabatar don ba Iran izinin samar da sinadarin uranium a cikin Rasha. Kasashen yamma karkashin jagorancin Jamus da Faransa da Birtaniya sun yi kira ga Iran da ta amince da wannan tayi, to amma gwamnati a Teheran ta dage kan cewar ita ma zata iya sarrafa uranium din a cikin kasarta. Rasha dai na kokarin kawo karshen kace-nace da ake yi tsakanin Iran da Amirka, wadda ke zargin Iran din da shirin kera makaman nukiliya a boye. Shugaba Mahmud Ahmedi-Nejad ya ce kasarsa zata fara aikin binciken sarrafa karafan nukiliya duk da barazanar da KTT da Amirka suka yi na mika Iran din a gaban kwamitin sulhun MDD don kakaba mata takunkumi.