Rasha da China sun ki a zartas da kuduri kan kasar Burma | Labarai | DW | 13.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha da China sun ki a zartas da kuduri kan kasar Burma

Kasashen Rasha da China sun hau kujerar naki don adawa da wani daftarin kuduri da Amirka ta gabatar a gaban kwamitin sulhu da nufin kawo karshen dambaruwar siyasa a kasar Burma dake kudu maso gabashin Asiya. Kasahen biyu masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun sun hana zartas da wannan kuduri na tarihi wanda aka tsara da zumar matsawa gwamnatin mulkin sojin kasar ta Burma lamba da ta saki dukkan firsinonin siyasa tare da kawo karshen cin zarafin mata da sojin kasar ke yi. Amirka ta yi kiyasin cewa kimanin firsinonin siyasa dubu daya da 100 ake tsare da su a Burma, ciki har da shugabar adawa Aung San Suu Kyi wadda ake yiwa daurin talala a gidanta.