1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha da China sun ƙulla yarjejeniyar cinikayya

March 22, 2006
https://p.dw.com/p/Bv4G

ƙasashen Rasha da China sun sanya hannu a kan wata yarjejeniya ta shimfida manyan bututu guda biyu don samar da iskar gas daga Rasha zuwa ƙasar China. Shugaban kamfanin Gazprom na iskar gas ta ƙasar Rasha, ya shaidawa manema labarai a birnin Beijin, cewa bututun za su fara samar da iskar gas daga Siberia zuwa ƙasar Sin nan da shekaru biyar masu zuwa. An ƙulla yarjejeniyar ce a yayin ziyarar kwanaki biyu da shugaban ƙasar Rasha Vladimir Putin ya kai zuwa ƙasar Sin, inda ya gana da shugaban ƙasar Hu Jintao. A yayin ganawar, shugabanin biyu sun yi alƙawarin ƙarfafa huldar dangantaka a tsakanin su musamman ta fuskar siyasa dana tattalin arziki.