1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ba za ta shiga binciken guba ba

Gazali Abdou Tasawa
April 4, 2018

Kasar Rasha ta zargi jami’an leken asirin Birtaniya da Amirka da bayar da guba ga tsohon jami’in leken asirinta Sergei Skripal wanda da farko aka zargeta da aikatawa. Cibiyar bincike ta Birtaniya ta ce bata gano kasa ba.

https://p.dw.com/p/2vU9n
UK Salisbury Untersuchung Nervengasanschlag Skripal
Jami'an bincike kan gubar da ta haddasa takaddama da RashaHoto: picture-alliance/PA Wire/B. Birchall

Hukumar yaki da yaduwar sinadarai masu guba a duniya, wadda ta zauna a birnin Hague a yau Laraba, ta ce Rasha ta gaza samun rinjayen da ake bukata a binciken zargin amfani da guba kan tsohon jami'in diflomasiyyarta a Birtaniya. Ta dai sami kuri’u shida ne, inda wakilai 15 suka ki kada kuri’unsu, kamar yadda majiyar jami'an diflomasiyyar ta fada wa kamfanin dillancin labaran Reuters.

A ranar hudu ga watan Maris din da ya gabata ne dai aka iske tsohon jami'in leken asirin kasar ta Rasha Serguei Skripal da diyarsa Yulia rai kwakwai mutu kwakwai a saman wani banci na wani wurin shakatawa a birnin Salisbury da ke a Kudu maso Yammar London. Bayan gudanar da bincike a kansu likitoci suka tabbatar da cewa mutanen biyu sun ci guba ne. A ranar 12 ga watan Maris binciken farko na 'yan sanda ya gano cewa an yi amfani ne da wani sinadari mai suna Novitchok da ke tauye nunfashi da aka kirkiro a Tarayyar Soviet a shekarun 1970-zuwa 1980. Wannan ta sanya ba tare da bata lokaci ba gwamnatin Birtaniya ta dora alhakin wannan aika-aika ga gwamnatin kasar Rasha. Lamarin da ya haifar da rikicin diflomasiyya tsakanin Rashar da wasu kasashen Turai da ta kaisu ga korar jami'an diflomasiyyar kasashen juna.

Großbritannien Friedhof in Salisbury | Untersuchung Grab von Ludmilla Skripal
Hoto: Reuters/P. Nicholls

To saidai kuma ga bisa dukkan alamu Birtaniya da sauran kasashen Turai sun yi riga malam masallaci ne wajen zargi da kuma daukar matakin diflomasiyyar da suka yi kan kasar ta Rasha dangane da wanann batu, domin kusan ba zato ba tsammani ne a ranar Talata, cibiyar bincike da gwaje gwaje ta kasar Birtaniya da aka dora wa nauyin gudanar da bincike kan sinadarin gubar da aka yi amfani da shi kan tsohon jami'in leken asirin  Rashar da 'yarsa ta sanar da cewa a binciken da ta gudanar ba ta samu hujjojin da ke tabbatar da cewa sinadarin gubar ya fito ne daga kasar Rasha ba. A kan haka ne ma kasar Rasha ta yi kira a wannan Laraba taron gaggwa na hukumar yaki da yaduwar makamai masu guba domin neman kasashen da suka zargeta da su ba ta amsa kan wannan batu domin kauce wa fadawa abin da ta kira sabon rikicin diflomasiyya irin wanda ya hada Rasha da Amirka a kasar Kuba da ya nemi kai kasashen ga gwabza yaki a shekara ta 1962. Kuma Ministan harakokin wajen Rasha Sergei Lavrov  ya bayyana cewa a shirye Rasha ta ke ta mayar da martani kan masu yi mata wannan zargi:

Sergej Lawrow
Sergej Lawrow ministan harkokin wajen RashaHoto: Getty Images/AFP/J. Macdougall

"Komai zai zama kwatankwacin abin da aka yi mana, game da maganar jakadun da suka zama a nan haka batun ya ke a yanzu."

Sai dai duk da haka  da alama Birtaniyar na ci gaba da kafewa kan zargin da take yi wa Rashar kamar dai yadda  Sakataren harakokin Birtaniya Boris Johnson ya nunar a wata hira da ya yi da tashar DW: 

"Wanda suka yi wannan laifi ba al'ummar kasar Rasha ba amma kuma dole ne a samu wanda ke da hannu, mu a nan Birtaniya muna tunanin shaidun da aka bayar na nuni da cewar hukumomin Rasha na da hannu kuma Putin ne ke jagorantar gwamnatin kasar, don haka ba za a ce ba shi da hannu a wannan lamari ba."

Ita ma dai kasar Amirka wacce ke daya daga cikin kasashen da suka shiga takun saka da kasar Rasha kan wannan batu ta bakin sakatariyar harakokin wajenta Heather Nauert jaddada zargin nata ta yi kan kasar Rasha. Rasha dai ta nemi a gudanar da binciken bai daya tare da kwararrunta.