1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasa rayuka a Kamaru lokacin kidaya kuri'u

October 10, 2011

Babbar jam'iyar adawar kamaru ta rasa daga cikin magoya bayan ta lokacin da ake ci gaba da kidaya kuri'un da aka kada.'Yan takara 22 suka kalubalanci Paul Biya mai barin gado a zaben shugaban kasa mai zagaye daya tilo.

https://p.dw.com/p/12p7E
Magoya bayan SDF mai adawa a lokacin yakin neman zabeHoto: dapd

Jam'iyar SDF mai adawa a kasar kamaru ta zargi takwarta ta RDPC ko CPDM da ke kan karagar mulki da kashe daya daga cikin wadanda suka sa mata ido a zaben shugaban kasa da ya gudana ranar lahadi. Cikin wata sanarwa da jam'iyar ta fitar a wannan safiya, ta ce magoya bayan jam'iyar Paul Biya sun yi ma Virginie takoguem kisar gilla a garin Bandjoun da ke yammacin kasar lokacin da ake kidaya kuri'u da aka kada, sakamakon yin tir da yunkurin arongizon kuri'u da ta yi.Dama dai ma'aikatar kula da harkokin ciki gida a Kamaru ta ruwaito cewar an kashe sojoji biyu a yankin Bakassi dake kudu maso yammacin ƙasar wanda dama ke fama da tashe-tashen hankula.

Ana ci gaba da ƙidaya ƙuri'un da masu zaɓe suka ka'ɗa jiya Lahadin a ƙasar Kamaru, wanda kuma ake sa ran shugaban ƙasar Paul Biya ne zai sami damar tsawaita mulkin sa na tsawon shekaru 29. Sai dai 'yan adawa sun zargi hukumomin da tsara magudin zabe domin bai wa Paul Biya mai shekaru 78 da haihuwa damar ci gaba da mulki. 'yan takara 22 ne dai suka kalubalanci shugaba mai ci yanzu a zaben shugabanci kasa mai zagaye daya tilo.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Halimatu Abbas