1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rarrabuwar kawuna game da zaɓar sabon shugaban ƙasar Jamus

February 19, 2012

Tattaunawa tsakanin Jam'iyyar CDU ta Angela Merkel da takwararta ta FDP ta fuskanci turjiya game da zaɓen sabon shugaban ƙasa.

https://p.dw.com/p/145kO
A demonstrator holds a sign supporting German politician Joachim Gauck as president, as he stands in front of the Chancellery in Berlin February 19, 2012. The heads of the Germany's government coalition parties meet in the Chancellery for talks about the successor to former President Christian Wulff in Berlin. The sign reads, "Citizens for Gauck". Reuters/Fabrizio Bensch (GERMANY - Tags: POLITICS TPX IMAGES OF THE DAY)
Jami'an ƙawancen gwamnatin JamusHoto: Reuters

Gwamnatin ƙawance haɗin gwiwa ta nan Jamus wadda Angela Merkel ke jagoranta ta faɗa cikin taƙadda da jam'iyyun dake cikin ƙawancen gwamnati a game da wanda za'a naɗa ya maye gurbin shugaban ƙasar Christian Wulff wanda ya yi murabus a ranar juma'ar da ta wuce. Rahotanni sun ce Jam'iyyar FDP ƙaramar abokiyar ƙawancen gwamnatin ta bada shawarar naɗa wani wanda ba ɗan siyasa ba Joachim Gauk mai shekaru 70 da haihuwa amma kuma Jam'iyyar CDU da Angela Merkel ta yi watsi da tayin. Shugabar gwamnatin Angela Merkel ta na da wa'adin lokaci zuwa ranar 18 ga watan Maris ta gudanar da taron majalisa ta musamman domin zaɓar wanda zai cike gurbin shugaban ƙasar. Shugabar gwamnatin dai ta nuna sha'awar zaɓo mutumin da dukkanin jam'iyyun za su amince da shi. Ita ma dai jam'iyyar adawa ta SPD ta yi kira ga Angela Merkel ta naɗa Gauk tsohon jami'in adana bayanan sirri na rundunar 'yan sandan kwamunist ta gabashin Jamus akan muƙamin na shugaban ƙasa.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Saleh Umar Saleh