Rantsar da shugaban farar hula a Myanmar | Labarai | DW | 30.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rantsar da shugaban farar hula a Myanmar

An rantsar da Htin Kyaw (Tin Chaw), na hannun daman Aung Sang Suu Kyi, wadda ta dade tana fafitikar ganin an mai da kasar bisa tsarin demokradiyya

Htin Kyaw (Tin Chaw) tsohon mai bata shawara ne kuma yake a jam'iyarta ta National League for Democracy. Htin Kyaw ya kasance shugaban kasa na farar hula na farko a kasar a cikin shekaru gommai. Sai dai rawar da zai taka a matsayin shugaban kasa ana gani bata wuce ta dan amshin shatan Suu Kyi ba, wadda dokar kundin tsarin mulkin kasar ya haramta mata zama shugaban kasa kai tsaye. A baya dai ta fito karara, ta bayyana cewa lallai ita za ta yi mulki daga bayan fage, an kuma rantsar da Aung San Suu Kyi a matsayin ministar harkokin waje.