Ana shirye-shiryen rantsar da sabuwar majalisar a Najeriya.
November 11, 2015Talla
Ana san ran cewar nan ba da jimawa bane shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai bada sanarwar kafa sabuwar majalisar zartawar kasar da ke jagaba ta fuskar tattalin arzikin kasa a nahiyar Afrika.
Bikin rantsarwar dai zai gudana ne a farfajiyar Aso Rock dake a Abuja fadar gwamnatin Najeriyan.
Ministocin dai sun hada da kwarraru daga fagage da dama na cigaban jama'a da mafiya yawan 'yan Najeriya suke ma kallon ko shakka babu kwaliya zata biya kudin sabulu.