Rantsar da sabuwar gwamnati a Finland | Labarai | DW | 19.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rantsar da sabuwar gwamnati a Finland

A yau ne aka rantsar da sabuwar gwamnatin kasar Finlöand,wanda ya kunshi mafi yawan mata a matsayin ministoci,sai dai wannan kasa dake tarihin bawa mata damar taka rawa cikin harkokin gudanarwa ta barwa maza jagorancin manyan maaikatau a hannun maza.

Sabuwar gwamnatin Prime minista Matti Vanhanen ,nada mata ministoci guda 12 ,a majalisar ministocin nasa guda 20,wanda ke zama na farkon irinsa a tarihin gwamnatocin kasashen duniya.

Shugaba Tarja Halonen,wadda ke zhama shugabar kasar Finland mace ta farko ,wadda ke shugabantar kasar tun daga 2000 nedai ta nada majalisar ministocin.Kimanin mata 84 suka lashe kujera a majalisar dokokin kasar mai wakilai 200,a zaben kasa daya gudana a watan daya gabata.

To sai dai muhimman maaikatu da suka hadar dana harkokin ketare da tsaro da kudi dama mukamin premier ya kasance a hannun maza,a kasar ta Finland.