Sabuwar majalisar zartaswar Najeriya
November 11, 2015Tun bayan da ya yi rantsuwar kama aiki a ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata, Shugaba Buhari ya mayar da hankali ne wajen yaki da masu almundahana da kudaden al'umma da kuma yakar kungiyar Boko Haram. Birgediya Janar Muhammad Mansur Dan-Ali ne dai aka ba wa ministan tsaro yayin da aka Geoffrey Onyeama ya samu mukamin minstan harkokin kasashen ketare. An dai ba wa Babatunde Fashola tsohon gwamnan jihar Lagos mukamin minstan makamashi da ayyuka da gidaje, yayin da aka nada stohon gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi a matsayin minsitan sufuri ita kuwa Kemi Adeosun ta samu mukamin ministar kudi. Fashola da Amaechi dai na zaman na kan gaba a jam'iyyarsu ta APC wajen tabbatar da ganin Buhari ya samu nasarar lashe mukamin shugabancin kasar. Ministocin na Buhari sun gaza na tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan, wanda ke da ministoci 42 a zamanin mulkinsa.