Rantsar da Ban Ki Moon a matsayin sakatare general na Mdd | Siyasa | DW | 14.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rantsar da Ban Ki Moon a matsayin sakatare general na Mdd

Ban Ki Moon

Ban Ki Moon

Sabon sakatare general na mdd Ban Ki Moon na kasar Koriya ta kudu da aka rantsar dashi a jiya,yayi bayyana halin da Darfur ke ciki da kasancewa wani babban balai,inda yayi alkawarin mayar da fifiko wajen kawo karshen zubar da jini a wannan yankin.

Mai shekaru 62 da haihuwa,kuma tsohon ministan harkokin wajen kasar ta koriya ta kudu,Ban Ki Moon,a ganawarsa ta farko da manema labarai bayan rantsar dashi a jiya a alhamis,yace halin da Darfur ke ciki ba abun amincewa bane ko kadan.

Yace zai tuntubi Kofi Annan mai barin kujerar a kjarshen wannan wata,adangane da hanyoyin warware rikicin na Darfur,musamman bisa laakari da irin kokarinsa wajen shawo kann gwamnatin Khartzum ta amince da tura dakarun mdd zuwa lardin na Darfur,domin maye gurbin na Afrika dake fama da karancin kayan aiki.

Mr Ki Moon ya jaddada cewa babu dole MDD tayi aiki kafada da kafada da kungiyar gamayyar Afrika Auda gwamnatin Sudan ,da wasu dake da alaka wajen warware wannan matsala.

A jawabinsa na karban wannan mukami kuwa,sabon jagoran MDD yayi alkawarin cigaba da gyaran majalisar,wadda yace tana fama da matsalolin cin hanci da rashawa da kuma nuna wariya da son kai ayan lokuta da suka gabata.

WA Kofi Annan mai barin gado kuwa,Ban Ki Moon cewa yayi.....Sakatare general Annan,inan matukar alfahari dacewa kaine zan maye gurbinka,a wannan matsayi daka bayyana da kasancewa mai kalubale matuka.Abun alfahari ne agare ni inbi sawunka"

Bugu da kari Mr Ki Moon yayi alkawarin farfado da martabar majalisar ta dunkin duniya ,tare da sanya tsanaki cikin harkokin gudanarwanta,bisa laakari da harkokin rashawa da suka muzanta shekarun karshen shekar 10 Kofi Annan akan wannan matsayi............

Kazalika ya jaddada cewa zai yi kokarin kare martaba da darajar wannan majalisa.Domin akwai bukatar dukkan maaikatantsa su mike tsaye domin aiki cikin gaskiya da adalci........

A jiyan ne ,kuma zauren majalisar ya martaba Kofi Annan adangane da irin muhimmiyaer rawa daya taka wajen warware rigingimun kasashe ta hanyar diplomasiyya.Kofi Annan mai shekaru 68 da haihuwa anashi bangaren,ya godewa membobin mdd 192,adangane da irin goyon bayan da suka bashi a shekarunsa na jagoranci.A ranar 31 ga watan da muke ciki nedai Annan zai sauka daga kujerarsa a hukumance,kana Ban ki Moon zai haye karaga a ranar 1 ga watan janairun 2007.