Rangadin ministocin Turai a Mali da Nijar | Labarai | DW | 02.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rangadin ministocin Turai a Mali da Nijar

Ministocin harakokin wajen Jamus da Faransa Jean Marc Ayrault da Frank-Walter Steinmeier sun isa a kasar Mali inda za su gana da Shugaban kasar kafin su zarce zuwa Nijar.

Jean Marc Ayrault da Frank-Walter Steinmeier sun jaddada shirin Kungiyar Tarayyar Turai na taimaka wa kasar da ma sojojinta a fannin yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda da ke ci gaba da addabar yankin Arewacin kasar.

A wannan Litinin, ministocin biyu za su gana da Shugaban kasar Malin Ibrahim Bubacar Keita a fadarsa sannan daga bisani su gana da shugabannin sojojin kasar ta Mali da kuma na rundunar tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali wato Munisma.

Daga nan kuma za su tashi zuwa birnin Gao na Arewacin kasar inda za su gana da sojojin Faransa na rundunar Barkhan kafin daga karshe su zarce zuwa birnin Yamai na Nijar inda a gobe Talata za su gana da Shugaba Mahamadou Issoufou da majalisar ministocinsa.