Rangadin Georges Bush a Latine Amurika | Labarai | DW | 09.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rangadin Georges Bush a Latine Amurika

Shugaba Georges Bush na Amurika, na ci gaba da ziyara aiki a yankin Latine Amurika, inda a yanzu haka ya yada zango a ƙasar Brazil.

Saidai jim kaɗan kamin saukar sa a birnin Sao Polo, saida dubunan jama´a su ka shirya zanga-zangar nuna ƙyamar Amurika.

Shugaba Bush zai anfani da wannan dama, domin sake farfaɗo da kwarjinin Amurika, a ƙasashen Latine Amurika.

Tare da shugaba Luna Da Sylva na Brazil, zai tanttana mussaman a kann batun tattalin arziki , hasali ma ,rikicin da ya ƙi ci, ya ƙi cenyewa a hukumar cinikaya ta dunia, wato WTO kokuma OMC, a game da tallafin da manoman Amurika ke samu daga gwamnati, wanda shugabanin kasashe matalauta ke ɗauka a matsayin ummal iba´isar karya tattalin arzikin ƙasashen su.

Bayan hulɗoɗin saye da yasarwa, shugaba Bush na da burin anfani da wannan ziyara, domin taka birki ga sabuwar hoɓa sarmar da ta kunno kai a yankin, bisa jagorancin shugaban Ugo Shavez na Venezuela dake matsayin babban mai adawa da manufofin Amurika.