1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bush Südkorea

Kujath, Peter / Tokio (NDR) August 5, 2008

Bush ya isa birnin Seoul a matakin farko na rangadin nahiyar Asiya

https://p.dw.com/p/EqqI
Masu zanga-zanga a Koriya ta KuduHoto: AP

Kwanaki uku gabanin buɗe wasannin Olympics a birnin Beijing na ƙasar China, a yau shugaban Amirka George W Bush ya isa birnin Seoul na ƙasar Koriya Ta Kudu a matakin farko na rangadin sa na ƙarshe zuwa nahiyar Asiya. Ƙololuwar wannan rangadi za ta kasance a Beijing inda shugaban na Amirka zai halarci bukin buɗe wasannin na Olympics a ranar Juma´a mai zuwa.


Da wataƙila yada zango da shugaban Amirka George W Bush ya yi a birnin Seoul gabanin ya zarce zuwa birnin Beijing don halartar bukin buɗe wasannin Olympics zai kasance cikin walwala, amma ya fuskanci fushin dubban masu zanga-zanga a babban birnin na Koriya Ta Kudu, waɗanda ke nuna adawa da yarjejeniyar sayarwa ƙasarsu naman shanu daga Amirka. Ɗaukacin ´yan Koriya Ta Kudu na fargabar cewa ana iya shiga musu da nama mai ɗauke da ƙwayoyin cutar haukar shanu. Ƙyamar Amirka tsakanin ´yan Koriya ta Kudu na dalilai masu yawa.


Ta ce "Za mu ci-gaba da gudanar da zanga-zanga har sai dakarun Amirka sun janye daga yankin tsibirin Koriya."


Amirka dai ta girke dakarun dubu 28 da 500 a yankin inda da yawa daga cikin al´ummomin yankin suka ce kasancewarsu na kawo ciƙas wajen yin sulhu da Koriya ta Arewa. Shirin nukiliyar Koriya Ta Arewa na daga cikin muhimman batutuwan da za a mayar da hankali kansu a tattaunawar da za a yi gobe tsakanin Bush da Lee Myung-bak. Bush zai kuma nemi mai yi masa masauki da ya sake tunani game da dakarun Koriya Ta Kudu a yankunan da ake fama da rigingimu.

Ƙololuwar rangadin ita ce Beijing, inda Bush zai kasance shugaban Amirka na farko da zai halarci bukin buɗe wasannin Olympics a wajen ƙasar Amirka. Bush ya dage kan cika alƙawuran da ya ɗaukawa shugabannin China a bara duk da cecekuce tsakanin Amirka da China. Batun da ake taƙaddama kansa shi ne na rikicin yankin Tibet da harkar hakan mai tsakanin China da Sudan sai kuma taƙaita ´yancin jarida a China. Bush ya yi fatali da Amirkawa da ke sukar wannan ziyara, inda ya ce ziyarar za ta ba shi damar ganawa ido da ido da takwaransa na China Hu Jintao inda zai taɓo muhimman batutuwa.


Ya ce "Ina jin muhimmin batu ga dangantaka tsakanin Amirka da China shi ne wannan tafiya da zan yi zuwa China. Ina ganin daidai ne a nuna mata cewa muna girmama ta, to amma ra´ayoyinmu sun bambamta a batutuwa da dama. Hanya mafi dacewa wajen ɗinke wannan ɓaraka ita ce ta diplomasiya"


Babban birnin Thailand wato Bangkok zai kasance matakin ƙarshe na wannan rangadi shugaban na Amirka mai barin gado.