1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya

June 20, 2006

Kasashen Turai suna kara toshe iyakokin su ga yan gudun hijira daga ketare

https://p.dw.com/p/BvTW
Yan gudun hijira daga Africa dake neman shiga Spain
Yan gudun hijira daga Africa dake neman shiga SpainHoto: AP

Nuna karimci ga baki babban abu ne da ake daukaka shi yanzu haka a nan Jamus. Jamusawa da baki daga ko ina cikin duniya, masu addinai da al’adu da asali iri dabam dabam, duk sun hada hannu wuri guda, domin shiga buibuwan wasannin kwallon kafa na cin kofin duniya dake gudana yanzu haka a kasar ta Jamus. Jamusawa sun gaiyaci yan wasa da yan kallo da masu sha’awar kwallon kafa zuwa kasar su, domin su shaidar da wannan gagarumin biki.

Wannan gaiyata ta Jamusawan tana tattare ne da sharadin cewar tilas ne bakin su koma kasashen su idan aka kare bikin wasannin na cin kofin duniya. Taken wasannin na cin kofin duniya a bana dai shine: bakunta tsakanin abokai. Sai dai kuma ko da shike ana marhabin da bakin: yan kallo, yan wasa da masu yawan bude ido, amma fa da zaran an kare wasannin su koma kasashen su: ba kuwa a wannan lokaci na wasannin cin kofin duniya kadai ba. Kasashen Turai da dama cikin su har da Jamus tun daga yan shekarun baya, sun sami nasarar toshe iyakokin su daga kwararar yan gudun hijira daga kasashen da ba na Turai din ba.

A lokacin yakin Balkan, kamar yadda ministan cikin gida, Wolfgang Schaeuble ya nunar, yan gudun hijira da masu neman mafakar siyasa dubu dari hudu ne suka rika shigowa nan Jamus a ko wace shekara, amma a bara, yawan yan gudun hijiran da suka shigo Jamus bai wuce dubu talatin ba. A kusan dukkanin kasashen Turai, an sami raguwar yawan yan gudun hijira dake kwarara daga ketare. Hakan kuwa ba wai yana faruwa ne saboda Jamus da kasashen Turai sun daina daukar hankalin yan gudun hijiran bane, amma sai saboda ganin yadda wadannan kasashen suka kara toshe iyakokin su.

Ko da shike yan gudun hijira masu tarin yawa har yanzu suna ci gaba da mafarkin samun damar zuwa Turai, amma yan kalilan ne a baya-bayan nan suke samun damar isa iyakokin kasashen kungiyar hadin kann Turai, inda suke fatan samun rayuwa mai armashi da jin dadi. Suma wadanda suka sami nasarar tsallaka iyakokin, duk da dimbin wahalolin dake tattare da hakan, suka shigo Turai, kai tsaye akan sake mayar dasu inda suka fito: wato ko dai a maida su kasar da suka fara yada zango cikin ta kafin su iso Turai ko kuma a maida su kasashen su na asali.

Jamus da kasashen Turai suna daukar kasashe masu tarin yawa a matsayin kasashe ne da yan gudun hijiran zasu iya zama cikin su, ba tare da sun ji tsoron rayuwa ko makomar su idan aka maida su can ba. Hukumomi a nahiyar Turai sukan nunar da haka, a duk lokacin da suka ki amincewa da takardun neman mafakar siyasa da dan gudun hijira ya gabatar. Wani lokaci ma zargin azabtarwa baya zama wani dalilin da zai sanya a amince da dan gudun hijira a matsayin mai neman mafakar siyasa saboda dalilai na siyasa ko addini.

Irin wadannan manufofi, wadanda aka amince dasu ta hanyar zabubbuka masu yawa, sau tari sukan nunar da tsoro ne dake zukatan al’ummar nahiyar Turai, wato tsoron maida kasashen na Turai wadanda baki zasu mamaye su, ko kuma tsoron cunkoson yan gudun hijira dake neman neman abin duniya ne kawai ko kuma tsoron samun koma-baya a tsarin rayuwa saboda yawan yan gudun hijiran.

To sai dai kuma suma mutanen dake tserewa daga kasashen su, sukan kasance cikin hali na tsoron shiga wani hali na tashin hankali ko rashin makoma mai kyau ko matsin lamba daga hukumomi a kasashen da suka shiga. Kazalika, yan gudun hijira masu yawa sukan kasance a cikin wani yanayi na rashin sanin tabbas ga makomar rayuwar su, har yadda ba zasu iya sakin jiki su nemi shimfida wata rayuwa ta kirki ba. Saboda haka ma taken ranar ta yan gudun hijira a bana, wato fatan ci gaba da kiyaye tsarin rayuwa, ya zama kamar cin mutunci ne ga yan gudun hijiran.

A daya hannun, yan gudun hijira da kasashen dake karbar su, suna iya cin gajiyar juna. Nahiyar Turai dai tana fama da matsalar tsufan al’umar ta da karancin hayaiyafa. Nahiyar tana bukatar kwararowar mutane daga ketare masu dauke da sabbin dabaru da karfin tafiyar da aiyukan yau da kullum. Yan gudun hijira dake shiga cikin mummunan hadari kafin su sami nasarar isowa Turai, suna iya bada gudummuwar da nahiyar take bukata domin ci gaba da rayuwa. To amma nahiyar tana kuma bukatar sabbin dokoki da zasu daidaita kwararan baki daga ketare, yayin da su kuma kasashen da yan gudun hijira suke tserewa daga garesu, suna bukatar daukar matakai domin baiwa al’ummar su kwarin gwiwa da damar ci gaba da zama a can.