Ranar yaki da miyagun kwayoyi ta duniya | Labarai | DW | 26.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ranar yaki da miyagun kwayoyi ta duniya

A yau ne ranar yaki da miyagun kwayoyi ta duniya,inda kasashen duniya suke kara maida hankali kann tuammali da kuma fataucin miyagun kwayoyi a duniya da kuma illarsa ga alummomin duniya da tattalin arzikinsu.

Wani rahoton shekara shekara na Majalisar Dinkin Duniya akan tuammali da miyagun kwayoyi data fitar yau, ya ce,an samu nasarar rage yawan tuammali da miyagun kwayoyi a duniya,sai dai zaa iya samun koma baya,muddin dai kasashen duniya basu ci gaba da wannan kokari da suka fara ba.

Shugaban hukumar yaki da miyagun kwayoyi na Majalisar, Antonio Maria Costa,yace akwai bukatar kasashen duniya su hada kai wajen yaki da miyagun kwayoyin ta hanyar bullo da kwarara manufifi akan fatauci da anfani da su,wanda yace hakan zai rage bukata da kuma samarda kwayoyin,