Ranar yaki da cutar Malaria a duniya | Labarai | DW | 25.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ranar yaki da cutar Malaria a duniya

Yau a ko ina a fadin duniya ake gudanar da bikin ranar yaki da cutar Malaria ta zazzabin cizon sauro. Hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF ta bukaci kasashe su kara bada himma wajen kawar da cutar daga doron kasa. Itama gwamnatin Jamus ta yi kira da babbar murya da a hada karfi wuri guda domin yaki da cutar Malaria wadda ke hallaka kusan mutane miliyan daya a kowace shekara. Ministan raya kasa da taimakon jin kai Heidemarie Wieczoreck-Zeul tace cutar wadda ana iya maganin ta, ta addabi jamaá a kasashe masu tasowa. Ta yi kakkausar suka da cewa idan da a kasashe masu cigaban masanaántu ta yadu da tuni an yi kokarin samar da Allurai da kuma magungunan cutar. Tace akwai bukatar tallafawa kasashen masu tasowa domin yaki da cutar ta Malaria. Ministan ta jamus zata jagoranci hadin gwiwar kasashen Turai domin fadakarwa a game da yaki da cutar ta zazzabin cizon sauro.