Ranar yaki da cutar kanjamau | Labarai | DW | 01.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ranar yaki da cutar kanjamau

Yau ne ranar da majalisar dinkin duniya ta kebe don yaki da cutar kanjamu a duniya.

Sakataren majalisar dinkin duniyar Kofi Annan yayi kira ga jamaa da su kara kaimin yaki da cutar ta AIDS.

Annan yace ya kamata a tuhumi shugabanin siyasa game da nuna halin ko in kula game da cutar.

Yace kwayar cutar wadda ta kashe mutane miliyan 25 wasu kuma miliyan 40 suke dauke da ita,itace babbar kalubale da aka taba fuskanta a wannan zamani.

Yankin Afrika dake kusa da sahara dai shine yanki da cutar tafi shafa,inda yanzu haka mutane miliyan 24 da dubu dari bakwai suke dauke da kwayar cutar HIV.