Ranar yaki da cutar Aids | Labarai | DW | 01.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ranar yaki da cutar Aids

Yau ne 1 ga watan desember, ranar da majilasar Dinkin Dunia ta kebe a fadi dunia baki daya, domin fadakarwa da yawo kanan al´umma a game da billa´in cutar Aids kokuma Sida, da ke ci gaba da daukar miliyoyin rayuka.

Rahoton kungiyar Majalisar Dinkin Dunia, mai kulla da wannan cuta ,ya sannar cewa fiye da mutane million 40 su ka kamu da kwayoyin ta, daga cikin su million 25 ,sun riga mu gidan gaskiya.

A shekara damu ke ciki, mutane million 3 su ka rasa rayuka sanadiyar cutar kabari sallamu alakaikum.

Kungiyar yaki da cutar, ta yi kira ga kasashe masu hannu da shuni, da kungiyoyin kasa da kasa da su cika alkawuran da su ka dauka, na tallafawa kasashe matalauta, domin su yaki wannan annoba.

A kasashen Afrika mutum daya rak, daga ciki ko wane mutane 10, da ke dauke da kwayoyin cutar, ke samun maganin rage raddadin ta.

Kungiyar na bukatar tattara a kalla dalla billiar 3 da rabi, domin fuskantar yakin a tsawan shekaru 2 masu zuwa.

Kiddidigar da wannan kungiya ta gudanar ta gano cewa a ko wace ranar Allah ta´alla, mutane dubu 14 ke kamuwa da cutar Sida.

Saidai duk da haka, an dan samu ci gaba a fadi ka tashin da a ke na dakile Aids, ta la´akari da raguwar masu kamuwa da ita a kasashen da ta fi kamari kamar su Kenya da Zimbabwe.