Ranar yaki da cin hanci da rashawa | Siyasa | DW | 09.12.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ranar yaki da cin hanci da rashawa

Yau ce ranar yaki da Cin hanci ta Majalisar Ɗunkin Duniya

default

Peter Eigen

9 ga watan Disamba na kowace shekara, rana ce da Majalisar Ɗunkin Duniya ta keɓe domin yaki da cin hanci da rashawa. Inda akan jera sunayen kasashe,da kamfanoni dama hukumomi, bisa ga irin matsayinsu a wajen harkokin da suka shafi cin hanci ko kuma karɓar rashawa.

A kowace shekara Transparency International ,wadda ke kasancewa kungiya mai zaman kanta ta kasa da kasa dake yaki da harkokin cin hanci da karɓar rashawa,itace ke gabatar da jerin sunayen kasashe na sukayi kaurin suna a cin hanci da a shekarar data gaba,bisa ga bincike da ta gudanar.Dr Peter Eigen shine ya kafa wannan Kungiyar ....

"Alal misali gwamanatin Jamus ta rasa yadda zatayi.Domin tayi nuni dacewa ,babu yadda zata san yadda manufofin mutane suke bisa ga yadda suke tafiyar da lamuransu,bisa la'akari da matsayinta a tsakanin kasashe"

A shekara ta 1993 nedai Peter Eigen ya kirkiro wannan kungiya ta Transparency International.A matsayin shi na tsohon ma'aikacin Bankin Duniya,yayi hulɗoɗi masu yawa da 'Yan siyasan kasashen Afrika da Asia da yankin Latin Amurka,waɗanda sukayi aiki tare a Bankin.

Daga wannan lokacin aka Kungiyar take da cibiyarta a birnin London,ayayinda Berlin ke zama cibiyar kula da cin hanci da rashawa.Peter Eigen yace kafa wannan kungiya nada nasaba da daɗewarsa da a Bankin duniya akarkashin harkokin da suka shafi Afrika....

"An bayarda ayyukan gima dam dam ,da bututun tuwa da hanyoyin jiragen kasa da filayen saukan jiragen sama,akan tsabar miliyoyin daloli,amma babu sakamako.Ayayinda akayi watsi da muhimman ayyuka masu yawa,wadanda kuma bazasu ci kudi ba kamar,gyaran makarantu da Asibitoci"

Jagoran Transparency yace Irin waɗannan matakai na siyasa suna da illa ga rayuwar kowace al'umma.....

"A nawa ra'ayin lokaci yayi da zaa yi watsi da irin wannan tsarin tattali na siyasa,inda zakaga a a kasashe masu yawa ,yara matasa basu da wata makoma,wanda kuma yakan sa su gwammace da shiga ayyukan tarzoma"

To sai dai ana samun sauyin matsayi a tsarin sunayen da akan jera a kowace shekara.Kasar Botswana dake yankin kudancin Afrika ala misali na ɗaya daga cikin jerin kasashen da suka samu cigaba a nahiyarmu ta Afrika.Alal misali,da albarkatun kasa da Allah ya huwace mata,ana samun tafiyar da ayyukan kwangiloli kamar yadda suka dace.To sai hakan zai iya dorewa ne kadai aidan akwai gaskiya da adalci a bangaren gwamnati inji tsohon shugaba Botswana Festus Mogae....

"Muna da zaɓaɓɓiyya kuma zaunanniyyar gwamnati,wadda aka zaɓa akarkashin doka.Yanzu idan rikici ya ɓarke zance tabbatar da gaskiya da adalci bazai wani tasiri ba.Waye zaka binciki takardunsa? Babu wanda zai yarda ka binciki ayyukansa,idanma suna da takardun dake kunshe da bayanai"Sauti da bidiyo akan labarin