1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ranar yaki da cin hanci da karbar rashawa

Yahouza SadissouDecember 9, 2005

Albarakacin ranar yaki da cin hanci da karbar rashawa hukumar Transparency International ta gabatar da rahoto

https://p.dw.com/p/Bu3U
Hoto: dpa

A rana irin ta yau, a ko wace shekara, Majalisar Dinkin Dunia ta ware, domin ta zamo,ranar yaki da cin hanci da rashawa, matsalar da a halin yanzu ta zama ruwan dare gaba dunia.

Albarkacin wannan rana hukumar kare hakokin bani adama da papatakar tabbatar da adalci, Tranparency International ta hido rahoto.

Shugabar hukumar Transparency International ce, Madame Huguette Labelle ,ta gabatar da wannan Rahoton a birinin London, na Britania, wanda a baki dayan sa ya kunshi bayyanai a game da al´amarin cin hanci da rashawa.

Rahoton ya bayyana cewa jami´un siyasa a kasashe daban daban na dunia, sun kasance, matsayin mattatarar ci hanci da karbar rashawa.

Hakan ta tabata, a sakamakon binciken da hukumar ta gudanar, a kasashe 45, daga jimilar kasashe 69 a dunia da binciken ya shafa, inji Huguette Labelle shugabar hukumar .

Idan a ka kwatanta da sakamakon binciken shekara da ta gabata, alkalluman cin hanci da rashawa sun a bainin jami´iyun siyasa.

Biciken na bara ya gano cewa kasashe 36 ne bisa 62 ke fama da wannan annoba, mai kame garkuwar tattalin arzikin kasahe mussaman masu tasowa.

Kiddidigar da hukumar ta gudanar na nuni da cewa matsalar ta fi shafar talakawa.Kashi 42 bisa 100 na yawan talakawan da a ka tambaya sun tabatar da su na fuskantar matsala fiye da kima, a bayangaren masu hannu da shuni kashi 36 bisa 100 su ka bayyana fama da ita a opisohi daban daban da su ka hada da na gwamnati da masu zaman kansu.

Kazalika kiddidigar ta gano kashi 57 bisa 100 wanda su ka shaidi cewa cin hanci da rashawa ya karu a tsawon shekaru 3, sannan kussan rabi na mutane dubu 55 da a ka tambaya sun bayana ra´ayoyin cewa matsalar zata karuwa nan da wasu shekaru 3 masu zuwa.

Daga cikin kasashe 8 na Afrika, da hukumar Transparency International ta gudanar da binciken na ta,ta gano cewa yan sanda ke sahun gaba ta fannin karbar cin hanci, sannan sai jam´iyun siyasa.

Kasashen da ke sahun gaba a nahiyar ta Afrika kuwa, sune Kamaru , Ghana da Nigeria.

Bayan yan sanda da jam´iyun siyasa, opisoshin da ke sahu na 2, sune Majalisun dokoki, kotuna shari´a, Duwan ko Custums, da kuma opisoshin karbar haraji.

Daga kasashe masu karfin tattalin arziki, da binciken ya gano cewar jam´iyun siyasa sun fi fama da al´amarin cin hanci da rashawa, akwai Jamus, Amurika, Kanada, Spain, Faransa, Italia Japan, Britania da Suizland.

A nan turai bayan jam´iyun siyasa, kafofin watsa labarai, da majalisun dokoki ke sahu na 2.

Rahoton na Transparency International, ya binciko cewa a halin da a ke ciki cin hanci da rashawa ya fara kutsawa a cikin makarantu, inda nasara da dallibi zai samu, ta daganta da dan abun goro, da zai ba mallumai.

Transparency ta bada missalin Jamhuriya Niger, Zambia Siera-Leone,, Geogia, Brazil ,da Argentina,a matsayin kasashen da su ka kazance wajen karbar cin hanci da rashawa a cikin makarantu.

Idan a ka yi la´akari da halin talauci da ya wa al´umomin wannan kasashe katutu, abin na da ban tsora kasancewar iyaye da dama, basu da halin bada kudaden cin hanci ga mallumai ko shugabanin makarantu, da sauran magabata, abin da babu shakka, zai jawo illar zaman kashe wando, ga yara da dama yayan talakawa.

Transpareny International a karshe, ta yi kira ga kasashe da al´ummomin dunia, da su tashi tsayin daka domin yakar cin hanci da rashawa.