Ranar yaƙi da zazzaɓin cizon sauro | Zamantakewa | DW | 25.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Ranar yaƙi da zazzaɓin cizon sauro

Ba a samu sakamakon a zo a gani ba, shekaru 10 da ƙaddamar da shirin rage yawan masu fama da zazzaɓin cizon sauro a duniya.

default

Nau'in sauron dake yaɗa ƙwayoyin cutar malaria

Kimanin shekaru 10 da suka wuce ƙasashe membobin Majalisar Ɗinkin Duniya sun ɗauki alƙawarin cewa kafin ƙarshen shekarar 2010, za su rage yawan mutanen dake kamuwa ko mutuwa sakamakon zazzaɓin cizon sauro wato Malaria ya zuwa rabinsu na yanzu. Ana buƙatar gidan sauro da kuma magunguna ga aƙalla kashi 80 cikin 100 na mutane a yankunan dake fama da cutar Malaria. Wannan shiri da aka yiwa laƙabi da "Shekaru 10 na kawad da Malaria" a bana ya ke kawo ƙarshe. To sai dai sakamakon da aka samu mai baƙanta rai ne domin ba a cimma wannan buri ba a ɗaukacin ƙasashen da aka tsara wannan shiri dominsu.

Har yanzu gidan sauro shi ne mafi inganci wajen yaƙi da yaɗuwar zazzaɓin cizon sauro. Kamata yayi a samar da gidajen sauron ga mutanen dake zaune a yankunan dake fama da cutar ta Malaria, domin rage yaɗuwar wannan cuta a duniya baƙi ɗaya. Gidan sauro ba ya da tsada amma ya na da inganci sosai inji Awa Marie Coll-Seck ta shirin yaƙi da Malaria na Ƙungiyar Lafiya Ta Duniya WHO.

"Ana samar da waɗannan gidajen sauro ne ta wata hanya ta musamman kuma suna kai shekaru uku zuwa biyar. Ana iya rage yawan yara 'yan ƙasa da shekaru 5 dake mutuwa sakamakon cutar Malaria da kimani kashi 25 cikin 100, sannan iya rigakafin kaifin cutar da misalin kashi 50 cikin 100. Alal misali a cikin shekaru biyu mun rarraba gidan sauro fiye da miliyan 20 a ƙasar Ethiopia, inda ta haka Malaria ta ragu da sama da kashi 20 cikin 100."

A cikin shirinta na kawad da Malaria cikin shekaru 10, har zuwa shekarar 2008, WHO da membobinta sun samar da gidan sauro kimanin miliyan 140 ga ƙasashen Afirka, kuma hakan ya taimaka wajen rage yawan yaɗuwar cutar.

To sai dai a jimilce sakamakon wannan shirin bai gamsar ba, domin har yanzu Malaria na zaman babban haɗari a ƙasashe 108, musamman a nahiyar Afirka, inda ƙasashen da suka samu nasarar rage yawan waɗanda cutar ke zama ajalinsu ba su haura guda tara ba. Rashin masaniya game da Malaria musamman kan amfani da gidan sauron na daga cikin dalilan da suka sa zazzaɓin cizon sauron ke zama gagarabadau a wannan nahiya, inji Awa Marie Coll-Seck.

"Akwai wuraren da ake amfani da gidan sauron don kamun kifi, musamman a ƙasashen da a baya ba su san yadda za su amfani da gidan sauron ba ko kuma ba su ba da amfani da shi ba. Saboda haka ya zama wajibi a garemu mu riƙa wayar da jama'a kai bisa manufar da aka sa a gaba."

Hatta a ɓangaren samar da magunguna ma kwalliya ba ta mayar da kuɗin sabulu ba domin duk da cewa an samu ƙarin yawan masu samun magungunan cutar ta Malaria amma mafi yawancin mutane ba sa samun magungunan yadda ya kamata. A binciken da aka yi a ƙasashe 13 na Afirka, a ƙasashe 11, ƙasa da kashi 15 cikin 100 na yara 'yan shekaru uku zuwa biyar ne suka samu magungunan Malaria. Bugu da ƙari rashin kyakkyawan tsarin kiwon lafiya a ƙasashe da dama na wannan nahiya na mayar da hannun agogo baya. A saboda haka ƙungiyoyin farar hula ke kira da a sake dubara a yaƙin da ake yi da zazzaɓin cizon sauro. Sussane Schmitz ta wata ƙungiyar agaji ta Jamus da ake kira Medeor dake wayar da kan jama'a a wani ƙauyne ƙasar Togo ta ce dole sai an haɗa ta matakai na tsabtace muhalli kafin a cimma burin da aka sa gaba.

"Da mu da ƙawayenmu mun gano cewa matakan da ake amfani da su yanzu ba sa wadatarwa, domin ba bu wani bincike ko sa ido na dogon lokaci don tabbatarwa ko mutane suna aiwatar da shirye shiryen. Saboda haka ƙawayenmu a Togo suna bi ƙauyuka suna shigar da mazauna a cikin aikin da muke yi."

Duk da ƙoƙarin da ake yi, ƙarancin kuɗi na ci-gaba da zama babbar matsala. Alƙalumman WHO sun nunar da cewa a duk shekara ana buƙatar dala miliyan dubu biyar domin yaƙi da Malaria to amma a cikin shekaru 10 na wannan shiri na ta, miliyan dubu 2.7 kaɗai WHO ta samu.

Mawallafa: Asumpta Lattus / Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadisou Madobi