Ranar yaƙi da jahilci | Zamantakewa | DW | 08.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Ranar yaƙi da jahilci

Albarkacin ranar yaƙi da jahilci UNESCO ta yi bitar inda a ka kwana game da wannan batu.

default

Ranar yaƙi da jahilci ta duniya

Kamar ko wace shekara,yau ne Takwas ga watan Satumba ranar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware domin faɗakarwa game da yaƙi da jahilci a matsayin matsalar da ke assasa talauci tsakanin al´umma.

Samar da ilimi ga ko wane mahaluki, a ƙarƙashin wannan taken ne, shekaru 10 da su ka gabata, ƙasashen duniya fiye da 160 su ka shirya zaman taron a  birnin Dakar na ƙasar Senegal.Sakamakon wannan taro, ya bayana wajibcin koyar da ilimin karatu da rubutu ga ko wane bani adama.To saidai rahoton shekara na Hukumar ilimi ta duniya wato UNESCO, ya ce a shekara da ta gabata akwai mutane miliyan 760 a duniya wanda ba su iya karantawa ba, kuma ba su iya rubutawa ba.Kusan dukan wannan jama´a na raye a  ƙasashen Afrika kudancin Sahara da yankunan kudu da yamacin Asiya.Rabi daga wannan addadin marasa ilimi na zaune a Ƙasashe huɗu, wato Bangladesh,China,Indiya da Pakistan.

To amma idan aka la´akari da matsayin shekaru 10 da su ka gabata an samu ci gaba ta fanin yaki da jahilci inji Katja Römer da ke cibiyar UNESCO reshen  Jamus:

"Duk da cewar akwai tafiyar hawainiya wajen cimma burin da aka sa gaba, an ɗan samu ci gaba.Daga shekara ta 2000 zuwa yanzu, an yi nasara ilimantar da mutane fiye da miliyan ɗari a ƙasashe daban-daban na duniya".

Hukumar UNESCO ta yaba da ƙoƙarin da aka samu  a ƙasar China inda shekaru 20 da suka wuce gwamnati ta shiryawa talakawa fiye da miliyan ɗari karatun yaƙi da jahilci.To sai dai a ɗaya wayjen akwai sauran rina kaba, musamman a wasu ƙasashe yankin kudancin Asiya da na Afrika kudu ga Sahara da ma wasu ragowar ƙasashen larabawa.Katja Römer ta bayana dalilan wannan koma baya:

"Babban dalili shine gwamnatin ba su maida hankali ba ga wannan batu.Abin taikaice ne, ganin yadda  a ƙasashe da dama wanda abin  ya shafa, magabata ba su ɗauki yaƙi da jahilci ba, a matsayin wata kafa ta samar da ci gaba, ahlali kuwa a zahirin gaskiya talakan da ya samu ilimi tamkar girka tubalin tushe ne na ci gaban ƙasa".

Itama Caroline Pearce ta Ƙungiyar Oxfam cewa ta yi samar da ilimin karatu da rubutu ga dattijawa kokuma matasan da ba su samu kafa shiga makaranta ba, ba ƙaramin taimako ne ba, wajen yaƙi da talauci:

"Ta fannin cigaban ƙasa,Kuɗaɗen  da ake kashewa wajen samar da ilimi, sun lunka har sau ukku, wanda ake kashewa ta wani ɓangare.Samar da ilimi na tafiya tare da kiwan lafiya.Misali a tarayar najeriya, Jamhuriya Nijar da Senegal, yawan yaran da ke mutuwa wanda iyayen mata ba su yi ilima ba sun lunka har sau biyu yawan yaran da ke rasuwa wanda iyayensu mata su ka samu ilimi".

A wani ɓangaren kuma, ƙiddidigar da UNESCO ta gudanar ta gano cewar kashi biyu cikin ukku na yawan mutanen da ba su iya karatu da rubuta ba, mata ne.

Mawallafi: Yahouza sadissou Madobi

Edita: Ahmad Tijani Lawal